Gwamnan jihar Yobe kuma shugaban kwamitin rikon kwarya na jam’iyyar APC, Mai Mala Buni, ya yi kira ga ‘yan takarar kananan hukumomi a jihar tare da Magoya bayansu da su gudanar da ayyukansu cikin kwanciyar hankali gabanin lokutan zabe.
Mai Mala Buni ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da Maitaimaki na musamman kan kafafan watsa labarai Mamman Mohammed ya sawa hannu.
Ya bukaci da Al’umma su zabi wanda ya dace a yayin gudanar da zabukan domin daurewar zaman lafiya a jihar.