fbpx
Wednesday, April 21
Shadow

Gwamna Tambuwal Na Jihar Sokoto Ya Umarci Manoma Da Su Koma Gona

Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sokoto ya umarci manoma da ke yankunan da masu garkuwa da mutane suka addaba da sukoma gonakinsu, tare da ba da tabbacin cewa gwamnatocin jihohi da tarayya suna aiki tare don maido da zaman lafiya ta kowane hali.

Gwamnan ya kuma yi kira ga al’ummomi da su ci gaba da jure ayyukan ci gaba da sojoji ke yi a yankunansu.
“Mun san yadda hakan ke da takurawa, amma ina baku tabbacin cewa yana cikin muradin mu gabadaya,” in ji shi.
Ya ce “Ba za mu iya zama a cikin yanayi da da manoma ba za su rika zuwa gona ba; kuma a karshen ranar, mu kasance muna fuskantar karancin abinci.
A cewar gwamnan, jihar ta samar da takin zamani da sauran abubuwan gona domin samun nasarar noman rani.
Gwamnan, a lokacin, ya yi taya musulmai a yayin bikin Ed-el-adha.
Ya yi kira ga jama’ar jihar, yayin bikin, su bi dukkan ka’idojin kare yaduwar cutar corona sannan su ci gaba da addu’a ga wadanda abin ya shafa.
Ya yaba wa rundunar yaki da cutar karkashin jagorancin kwamishinan lafiya, Dakta Ali Inname, da duk membobin kungiyar sa da kuma ma’aikatan kiwon lafiya da suka jajirce wajen yakar cutar.
“Dole ne mu ci gaba da fadakarwa kan wannan cutar.
“Har yanzu tana nan kuma muna bukatar mu yi taka tsantsan,” in ji shi.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *