fbpx
Sunday, March 7
Shadow

Gwamnan Jihar Abia, Ikpeazu mashayi ne – Sanatan Adeyemi

A cewar Adeyemi, yayin da yake ba da gudummawa ga wani kudiri kan kula da tsarin makaranta yadda ya kamata (Safe School Initiative) yace mashaya ne ke mulkin Jihar Abia.

Da yake mayar da martani ga wani sakon da aka yada ta kafar sada zumunta da ake zargin yana da nasaba da Sanata Enyinnaya Abaribe, wanda ya fito daga Abia, dan majalisar ya ce, “Duk da cewa wasu gwamnonin na iya bakin kokarinsu, mun yi sa’ar samun wani gwamna da ya dauki batun tsaro a matsayin babban abin da ya fi muhimmanci.

Yace Jihohi tara ne suke da iyaka da mu, amma mun sami gogewa game da munanan abubuwan da ke faruwa a jihohin makwabta.

Wasu Gwamnoni sun jajirce wajen kare mutanensu, kamar a jiha ta, Gwamna ya bayar da kwangilar gyaran makarantu tare da samar da igantaccen tsaro.

Ya kara da cewa, a wasu jihohin Nageriya ta nada mutane masu kaifin basira, masu ilimi sosai, masu kwazo sosai, kamar Abia, mashaya ne ke mulkar su.

Yacs Gwamnan Abia mutum ne mai shaye-shaye, a karkashin mulkin sa ya talauta mutanen Abia fiye da da.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *