Gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu ya baiwa fulani makiyaya dake dazukan jihar kwanaki 7 su fice daga cikinsu.
Hakanan ya haramta kiwo da dare nan take.
Gwamnan ya bayyana cewa daukar wannan mataki ya zama dole saboda yanda wasu bata gari suka mayar da dazukan jihar wajan aikata laifukan kisa, Satar mutane dan kudin fansa wanda hakan ke barazana ga zaman lafiyar jihar.
Gwamnan yace zasu baiwa makiyayan masu son zaman lafiya da kiwo ba da tada hankali ba damar yin rijista da hukuma.
“All Forest Reserves in the State are to be vacated by herdsmen within the next 7 days with effect from today, Monday 18th January 2021,” Akeredolu said.