Rahotanni sun bayyana cewa gwamnan Yobe, Mai Mala Buni ya auri matarsa ta 4 a asirce wadda kuma diyar Marigayi, tsohon shugaban kasa ne, Janar Sani Abacha, Watau Gumsu Fatima.
Sahara Reporters ta ruwaito cewar an yi aurenne a Abuja a karshen makon da ya gabata a a gidan Abacha.
Wani Hadimin Gwamnan ya gayawa majiyar cewa an yi aurenne a Asirce dan kada ya dauki hankulan jama’a. Gumsu me shekaru 45 a baya ta auri wani attajirin kasar Kamarune, Bayero Fadil Mahmoud.