Akalla mutane miliyan 6 tsakanin ‘yan shekaru 9 zuwa 44 ne za a yiwa rigakafin cutar zazzabin shawara a jihar Bauchi yayin da jihar ta fara aikin rigakafin kwanaki 10.
Jami’in rigakafin a jihar, Bakoji Ahmed shine ya bayyana hakan a ranar Juma’a yayin taron fadakarwa da aka gudanar na kwana daya kan Yaki da aikin rigakafin cutar Zazzabin shwara wanda aka gudanar a Cibiyar (EOC) dake jihar Bauchi.
Bakoji Ahmed ya bayyana cewa ba za a gudanar da aikin rigakafin ba a unguwanni 30 na kananan hukumomin Alkaleri, Kirfi, Bauchi da Tafawa Balewa saboda a cewarsa an gudanar da rigakafin tun a shekarun baya na shekarar 2019 da 2020 inda ya nanata cewa ana yin rigakafin ne sau daya kawai.