fbpx
Sunday, March 7
Shadow

Gwamnatin jihar Kano ta bayar da kwangilar biliyan N1 don samar da magudanar ruwa, da fitilun haskaka tituna a jihar

Gwamnatin jihar Kano ta bayar da kwangilar magudanan ruwa da sanya wutar haskaka titi a kananan hukumomi biyu na jihar.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ofishin kula da filaye ya fitar a ranar Talata, dauke da sa hannun kakakin ta, Auwal Ado.
Ya lissafa wasu daga cikin ayyukan da suka hada da samar da magudanan ruwa da tiles din da za a sanya a karamar hukumar Bichi.
Sanarwar ta ce magudanan ruwa da tiles din za su rufe hanyar da ta hada Sanka Quaters da ke Kofar Sidi Ahmed, Kofar Dan Iya Aminu da Kofar Wambai a Bichi.
Haka kuma sanarwar ta ce gwamnatin ta bayar da kwangilar samar da fitilun kan titin Faransa zuwa Zungeru, da titin Lamido da sauransu a cikin garin na Kano.
Sanarwar ta ce babban sakataren ofishin, Muhammad Yusuf ne ya sanya hannu kan yarjejeniyar a madadin gwamnati, yayin da Aliyu Ibrahim ya sanya hannu kan kwangilar, Tiamin Multi-Service Global Limited.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *