Rahotanni daga jihar Kano.
Gwamnatin jihar Kano ta tabbatarwa da BBC cewa za’a gudanar da Mukabala tsakanin Malaman jihar Kano da Shehin Malami Abduljabbar kamar yadda kwamishinan yada labarai a jihar Muhammad Garba ya bayyana.
Gwamnatin jihar ta sanya ranar 7 ga watan Maris a matsayin ranar da ta saanya domin gudanar da Mahawarar.