Kwamishinan harkokin tsaron cikin gida na jihar Zamfara, Alhaji Abubakar Dauran ya tabbatar da satar dalibai mata 300 a jihar.
Da yake magana da manema labarai yace yanzu haka yana kan hanyar zuwa Jangebe dake Talatar Mafara inda aka sace daliban.
Yace sun muma aika jami’an tsaro dan bin sahun wanda suka sace daliban, ya kuma bayana cewa ba zai iya fadar yawan daliban da aka sace ba sai ya je makarantar Tukuna.
Wasu majiyoyi sun bayyana cewa an sace dalibai da suka kai 300.