Ana fargabar mutane sun mutu a wani mummunan hatsarin mota wanda ya faru a ranar Asabar a Akungba-Akoko, hedkwatar karamar Hukumar Akoko dake Kudu maso Yamma a Jihar Ondo.
Duk da cewa ba a iya tantance adadin mutanen da suka mutu ba, amma rahotanni sun bayyana cewa dalibai da ‘yan kasuwa ne hatsarin ya rutsa dasu.
Wani dalibi ne ya tabbatar da hakan, Bolatito Arogundo, wanda yayi magana ta wayar tarho.
Ya shaida cewa lamarin ya faru a sakamakon birki da ya kwace wa wata mota lamarin da ya sanya motar afkawa kan wasu shaguna.
Sai dai harzuwa wannan lokaci Jami’an hukumar kiyaye haddura ta kasa (FRSC) ba su kai ga tabbatar da faruwar lamarin ba.