fbpx
Sunday, April 18
Shadow

Hadarin Mota ya rutsa da Shanu 12, an yanka 10, 2 sun mutu a Kaduna

Wani Hadarin Mota ya rutsa da shanu 12 a garin Sigau dake karamar Hukumar Lere ta jihar Kaduna.

 

Lamarin ya farune da yammacin jiya, Juma’a inda yaro me kiwon shanun ya je tsallaka titi dasu.

 

Saidai wani me babbar mota da ya taho da gudu ya kasa rike motar tasa inda ya bi ta kan shanun. Guda 12 ne suka jikkata inda aka yi gaggawar yankasu, saidai 2 sun mutu.

 

Wani Shaida ya bayyanawa Hutudole cewa babu mutum ko daya daya jikkata a hadarin.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *