fbpx
Sunday, April 18
Shadow

Hadimin Ganduje baya hannunmu>>Hukumar DSS ta musanta ikirarin kama shi

Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta musanta cafke mai taimaka wa Gwamna Ganduje na jihar Kano, Salihu Tanko Yakasai kan kalaman da ya yi a kan gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da jam’iyyar APC mai mulki.

Salihu Tanko-Yakasai, ya yi kira ga gwamnatin da Shugaba Muhammadu Buhari ke jagoranta da ta magance ‘yan fashi a cikin kasar ko kuma ta yi murabus.
Wani rahoto ya fito a ranar Asabar cewa an kama shi.
Amma Daraktan DSS na jihar, Muhammad Alhassan ya shaida wa manema labarai cewa, “ba mu kama ko ma mun gayyaci Salihu ba, kar ku manta shi abokinmu ne, wani lokacin, yana ba mu shawara kan al’amuran da suka shafi mawuyacin halin tsaro a Kano”.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *