Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya bayyana cewa ya kamata kwararrun mutane su rika shiga siyasa.
Yace sai an shiga siyasa ne sannan za’a iya kawo canjin da ake nema. El-Rufai ya bayyana hakane a wata hira da aka yi dashi a Legas.
Ya bayyana cewa, kada kwararru su rika zuwa suna aiki da kamfanoni masu zaman kansu, abinda ya kamata shine su rika shiga siyasa ana damawa dasu.
Yace zanga-zanga babu inda zata kai mutum, abinda ya kamata shine ya shiga siyasar ayi dashi.