fbpx
Sunday, March 7
Shadow

Haren-haren Boko Haram da ‘yan bindiga ya ragu sosai>>babban hafsan sojojin sama, Sadique Abubakar

Shugaban hafsan sojojin sama, Air Marshal Sadique Abubakar ya ce an shawo kan hare-haren da ‘yan bindiga da boko Haram ke kaiwa a arewa maso gabas da kuma’ yan fashi a yankunan arewa maso yamma da arewa ta tsakiyar kasar.

Da yake jawabi a wajen bikin yaye wasu jami’ai na kwasa-kwasan kwararru a cibiyar horas da sintiri a jihar Kaduna ranar Asabar 23 ga watan Janairu, Abubakar ya ce an samu wannan nasarar ne ta hanyar hadin gwiwar sojojin sama da na kasa da kuma sauran rundunonin tsaro, da kuma tura kwararrun jami’ai da kayan aiki.

 

Babban hafsan sojan saman wanda ya bayyana cewa Sojojin saman Najeriya a karkashin jagorancinsa sun bijiro da cigaban karfin kariyar Sojoji a yayin da ake samun karuwar yanayi na barazanar zamani, ya kara da cewa wannan ya zama dole a himmatu wajen daukar sabbin ma’aikata da kuma horar da jami’an rundunonin.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *