Kungiyar ISWAP da ta balle daga Boko Haram ta nuna hotunan wata kotar yaki data kwace daga hannun Sojojin Najeriya.
A sanarwar da ISWAP ta fitar a yau, Litinin, ta bayyana cewa ta kwace motar ne a wani harin kwantan bauna da ta kaiwa sojojin a yayin da suke daidai Gorigi, jihar Borno.
Kungiyar ta kuma yi ikirarin cewa ta kashe sojoji 20, kamar yanda Sahara Reporters ta ruwaito.