Da safiyar ranar Asabar ne Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya Halarci Taron Saukar Karatun Al-Qur’ani Mai Girma na Makrantar Maryam Ado Bayero (Mai Babban Daki) dake unguwar farawa a karamar hukumar Kombotso a jihar Kano.
Makarantar wacca tai bikin saukar Dalubai kimanin 40 wanda aka gudanar da bikin saukar a harabar makarantar dake unguwar Farawa.