Wani kamfani a Minnesota dake kasar Amurka yayi ikirarin samar da dan kamfai dake wanke kansa.
Kamfanin yace za’a iya saka dan kamfai din tsawon makonni ko watanni ba tare da an wankeshi ba, sannan kuma ba zai yi wari ba.
Hercleon kamfanine da a baya yayi riga da safa wanda ba sai an wanke su ba, a wannan karin yayi dan kamfai din da ba sai an wankeshi ba. Yana amfani da wasu kayane dake yaki da duk wata karamar cuta. Abinda kawai ake bukata bayan mutum yayi amfani da dan kamfan shine ya cire ya shanya na dan lokaci ya sha iska sannan ya dauko ya sake sakawa.