Sojojin Najeriya sun kashe Boko Haram 5 a wani hari da suka kai maboyar su dake Abbagajiri dake karamar hukumar Damboa ta jihar Borno.
Lamarin ya farune a ranar 20 ga watan Janairu kuma sojojin dake Rundunar Operation Tura ta kai Bango ne suka kai harin.
A harin wasu Boko Haram da dama sun tsere kuma sojojin sun kwace makamai da dama.