Hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Oyo (OYRTMA) ta cafke akalla mayaudara hudu wadanda ke nuna kansu a matsayin jami’ai masu kula da ababen hawa a karamar hukumar Ibadan ta Kudu maso Yamma tare da damfarar mutanen da basu ji ba su gani ba.
Da yake gabatar da su a hedkwatar hukumar da ke Ibadan a ranar Talata, 2 ga Maris, Shugaban Hukumar, Mogaji (Dokta) Akin Fagbemi ya shaida wa manema labarai cewa wadanda ake zargin sun yi karyar karbar kudi daga Naira dubu goma zuwa talatin da biyar (# 10,000) – # 35,000) saboda laifuka daban-daban.
Da yake magana, OYRTMA Boss ya ce za a mika wadanda ake zargin ga hukumomin tsaro da suka dace domin ci gaba da bincike da kuma hukunta su.