fbpx
Saturday, March 6
Shadow

Hukumar Sojin Najeriya ta karyata Tsohon Gwamnan Ekiti, Fayose kan harin Borno

Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose ya bayyana cewa abinda ya fada ya fito fili na cewa shugaban kasa, Muhammadu Buhari ba zai iya mulkar Najeriya ba.

 

Ya bayyana cewa harin da Boko Haram ta kaiwa Sojojin Najeriya har ta kori gaba dayan sansanin sojojin irin salon mulkin shugaba Buhari ne da Kuma Kwamandojin sojojinsa da suka gaza.

Saidai a martani ga wadannan kalaman nasa, Hukumar Sojin Najeriya ta bayyana cewa ba gaskiya tsohon gwamnan ya fada ba.

 

Hedikwatar tsaron Najeriya dai ta musanta cewa Boko Haram ta kwace sansaninta dake Marte inda tace Boko Haram din sun kai musu hari amma sun dakileshi.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *