Hukumar sojojin Najeriya na neman sojoji 101 da suka tsere daga New Marte da Dikwa yayin gwabzawar da suka yi da Boko Haram.
Kwamandan Rundunar Lafiya Dole ya kuma nemi a kulle Asusun ajihar Banki na sojojin har sai sun koma bakin aiki.
Peoplesgazette ta samo sunaye da kuma mukaman sojojin da suka tsere wanda aka ika Abuja da nufin kulle Asusun Ajiyarsu da kuma kamosu.
Boko Haram sun kaiwa tawagar 153 Taskforce Battalion hari wanda bayan gumurzu a Marte, Sojojin suka tsere, kamar yanda Rahoton ya bayyanar. Saidai daga baya shugaban sojojin Najeriya Maj Gen I Attahiru ya baiwa sojojin awanni 48 su kwato garin wanda kuma haka aka yi.
Boko Haram sun kuma sake kai hari Dikwa inda suka sace mutane.