fbpx
Tuesday, March 9
Shadow

Hukumar ‘yansanda ta sallami ‘yansandannan 2 da suka yi fada a tsakiyar titi daga aiki

Hukumar ‘yansanda Najeriya ta bayyana cewa ta sallami 2 daga cikin ma’aikatanta da suka yi fada a bainar jama’a a jihar Edo.

 

Ranar Alhamis ne dai Bidiyon fadan ‘yansandan ya watsu sosai a shafukan sada zumunta inda aka gansu suna kici-kici da juna.

 

Saidai dalilin fadan bai bayyana ba inda wasu dai sun rika zargin cewa kan rabon kudin cin hanci ne.

 

A sanarwar data fitar ta shafinta na sada zumunta, hukumar ‘yandasandan ta bayyana cewa an kama ‘yansandan masu sunan Ozimende Aidonojie da Salubi Stephen wanda ake kan bincikensu kuma za’a sanar da matakin da aka dauka akansu.

 

A sakamakon data fitar kuma daga baya,hukumar ‘yansandan ta bayyana cewa, ta dauki matakin korar  ‘yansandan biyu dsga aiki saboda abin kunyar da suka jawo mata.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *