fbpx
Sunday, March 7
Shadow

Jami’ar Nsukka ta dakatar da wani malamin da ake zargi da yi wa wata daliba ciki tare da yi mata barazana

Jami’ar Najeriya, Nsukka (UNN) ta dakatar da malamin ta, Dr. Chigozie Odum, da ake zargi da yiwa wata daliba ciki da kuma yi mata barazana.

An bayyana cewa, Dr. Odum, wani babban malami a Sashin Archaeology and Tourism, Faculty of Arts, ana zarginsa da yiwa wata daliba mai suna Onah Chinyere ciki.

Ance Dokta Odum Jude ya bukaci ya kwana da dalibar kuma ya yi mata barazanar cewa idan ta ki, ba za ta taba kammala karatun ta a sashen ba.

Ana kuma zargin cewa ya yi wa dalibai hudu ciki cikin shekaru 4 da ya fara Koyarwa a jami’ar.

An tabbatar da dakatar da Dakta Odum ne a wata wasika mai kwanan wata Litinin, 15 ga Fabrairu, 2021 kuma sa hannun Mataimakin Magatakardar jami’ar, Misis Achiuwa F.C.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *