fbpx
Sunday, April 18
Shadow

Ka koma makaranta ka koyi yadda ake magana – PDP ta gayawa Gwamna Lalong

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta fadawa gwamnan Filato Simon Lalong da ya “koma makaranta ya koyi yadda zai yi magana” kan rikicin manoma da makiyaya a jihar.

Gwamnan, a cewar jam’iyyar adawar, ya yi karya a kan maganar tasa kuma yana bukatar komawa makaranta kan yadda za a yi magana mai kyau a kan irin wadannan batutuwan masu matukar muhimmanci.

Lalong, yayin wani shirin talabijin a ranar Talata, ya ce rahotannin tsaro da ke hannun sa sun nuna cewa makiyaya da manoma duk suna dauke da bindigogin AK 47 domin su kare kansu.

Amma PDP ta yi daidai da sharhin Lalong, inda ta nemi ya bai wa manoma da mutanen jihar Filato hakuri saboda sayar da su, kuma ta bukaci da ya koma makaranta ya koyi yadda ake magana game da irin wadannan al’amura.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *