Shehin malamin addinin Islama, sheikh Dahiru Usman Bauchi ya bayyana cewa Fulani su bar garkuwa da mutane da Fashi.
Yace amma fa kada wani ya yaudaresu, su bar Garkuwa da mutanen su shiga Izala, yace saboda Izala ta fi Garkuwa da mutane muni saboda ita basa son Annabi.
Hakan ya bayyana ne a wata hira da aka yi da shehin Malamin wadda ta rika yawo a shafukan sada zumuna.
Sheikh Dahiru Bauchi yace shiga Izala idan suka bar Kidnapping kamar tsallen Badakene, ko kuma su fita daga Tabo su shiga kashi.