fbpx
Sunday, March 7
Shadow

Kasar Amurka ta gargadi China kan takurawa Musulmai

A karon farko tun bayan darewa shugabanci a watan jiya, shugaba Biden na Amurka ya yi magana da takwaransa na China Xi Jinping.

Fadar White House ta ce Mista Biden ya nuna damuwa kan fadada ikon Beijing a Hong Kong, tare da gargaɗin shugaban a kan yadda gwamnatinsa ke takurawa musulmin Uighur a jihar Xinjiang.

Sun kuma yi musayar ra’ayi kan canjin yanayi da haɓakar makaman nukiliya.

Dangantaka tsakanin manyan ƙasashe biyu masu ƙarfin tattalin arziki a duniya ta yi tsamin da bata taba yi ba.

Lokaci na karshe da shugaban kasashe Amurka da China suka yi magana kai tsaye shi ne a watan Maris din shekarar da ta gabata.

A bayan bayan nan ne BBC ta samu muhimman shaidu da ke bayyana yadda ake yi wa mata fyade da azabtarwa a sansanonin killace Musulmai ƴan ƙabilar Uighur.

Matan, wadanda suka ce an tsare su a sansanin tsawon watanni, sun ce ana azabtar da su da ƙarafan lantarki.

Sun kuma bayyana wani abin da ya faru lokacin da aka tilasta wa kimanin fursunoni 100 kallon wata budurwa da jami’an tsaro suka yi wa fyaɗe a gabansu.

A cikin wata sanarwa, gwamnatin China ta ce ta duƙufa wajen kare ‘yancin mata.

Kungiyoyin kare hakkin ɗan adam dai sun ce kusan Musulman Uighur 500,000 ne ake tsare da su.

Ita dai China a kullum tana musanta zargin da ake yi mata na gallaza wa Musulman, inda take cewa tana ilmantar da su ne a wasu sansanoni na koyar da sana’o’in hannu domin raba su da aƙidar tsananin kishin addini.

BBChausa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *