fbpx
Sunday, April 18
Shadow

Kotu ta umarci kakakin yan sandan Jihar Kano da ya biya diyyar N1m saboda kame wani dan gwagwarmayar tare da azabtar da shi ba bisa ka’ida

Babbar Kotun Tarayya da ke zaune a Kano a ranar Alhamis ta umarci mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar Kano, Abdullahi Haruna, da ya biya diyyar Naira miliyan daya a kan kame dan gwagwarmayar a shafukan sada zumunta, Bashir Galadanchi ba bisa ka’ida ba.

 

Bashir Galadanchi

Dan Gwagwarmayar yayi wani rubutu a facebook inda ya rubuta “Tsintacciyar mage bata mage”, wanda hakan yasa Kakakin yayi tunanin shi ne yake zagi, har ya kai ga sa a kame shi tare da azabtar da shi.

Mai Shari’a Obiora Egwuatu ya yi Allah wadai da abunda Kakakin ya aikata da kuma wasu jami’an dake da hannu akan cin zarafin da akayi wa matashin.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *