Hukumar Kula da Haraji ta Babban Birnin Tarayya Abuja (FCT-IRS) ta bukaci duk mazauna garin da su dinga biyan kudin harajin su a cikin lokaci, tana mai cewa hakan ita ce kadai hanyar da za ta iya mayar da garin kamar Dubai Singapore
A lokacin da yake zantawa da manema labarai a Abuja a ranar Lahadi, Shugaban Hukumar, Abdullahi Attah yace Abuja babban gari ne mai dajara, ya kara da cewa ta hanyar biyan haraji ne kaidai zai sa garin ya shiga jerin manyan birane duniya kamar Singapore da Dubai.
Dubai dai na daya daga cikin manyan garuruwan da ake yawon bude ido a fadin duniya.