fbpx
Sunday, April 18
Shadow

Ku daina shigo da shanu da kayan abinci a Kudu zamu iya siya a wasu wuraren – Kungiyar Afenifere

Sakataren Kungiyar Afenifere, Odumakin ya ce Arewa ba za ta iya yi wa Kudu barazana ta daina shigo shanu da sauran kayan abinci ba kasancewar akwai wasu wuraren da zasu iya siyan kayan.

Kungiyar Afenifere, ta ce yan Arewa za su iya janye shanunsu daga Kudu amma kada su manta cewa jihohin kudu sune da man fetur, wanda yana daya daga cikin tushen tattalin arzikin ƙasar.

Da yake magana a ranar Juma’a, Sakataren Yada Labaran kungiyar na kasa, Yinka Odumakin, ya ce akwai wasu hanyoyin samar da nau’in furotin (protein) ga ’yan kudu ba tare da sunci shanu ba.

Ya lissafa kasashe irin su Togo, Jamhuriyar Benin a matsayin kasashe masu sada zumunci inda Kudu za ta sayi shanu da sauran abubuwan da Arewa ta janye.

A cewarsa, janyewar kayan masarufi da Arewa za ta yi zai amfani yankin Kudu saboda hakan zai sa mutane su kara himma a harkar noma.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *