fbpx
Sunday, April 18
Shadow

Ku samar da tsaro a Makarantunku>>Shugaba Buhari ya gayawa Makarantu

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya jawo hankalin Makarantu masu zaman Kansu da guraren Ibada kan cewa su samar da tsaro a yankunan da suke.

 

Hakan ya biyo bayan sakin daliban Makarantar Kagara ta Jihar Naija wanda nan bada dadewa ba za’a sadasu da Iyalansu.

 

Gwamna Abubakar Bello na jihar Naija ya bayyana cewa daliban sun sha wuya a hannun wanda suka sace su din.

 

Saidai duk da wannan lamari, Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle ya sha Alwashin ci gaba da Sulhu da ‘yan ta’adda.

 

Shugaba Buhari yayi gargadin cewa Najeriya ba zata ci gaba da jure hare-haren da suke kawo mata matsala ba. Da yake magana kan sakin daliban Kagara, kakakin Shugaban kasa,  Malam Garba Shehu ya bayyana cewa shugaba Buhari zai ci gaba da nanata kiransa kqn makarantu da su ci gaba da samar da tsaro a yankunan da suke.

 

Ya sha Alwashin kamo tare da hukunta wanda suka aikata wannan lamari.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *