fbpx
Sunday, April 18
Shadow

Kungiyar Kiristocin Jihar Kwara ta yi tir da dokar sanya hijabi a makarantu Jihar

Kungiyar Kiristocin Najeriya reshen jihar Kwara ta yi tir da amincewar da gwamnatin jihar ta yi da amfani da hijabi da daliban mata Musulmi suka yi a makarantun gwamnati.

Sanarwar ta ce sabuwar manufar “za ta haifar da nuna wariya a makarantu tare da bai wa ‘yan ta’adda damar gano yaransu da kuma unguwannin cikin sauki”.

A ranar Juma’ar da ta gabata, gwamnati ta rufe makarantun Kiristoci 10 a Ilorin, babban birnin jihar, sakamakon tashin hankali kan sanya hijabi a makarantun.

Amma yayin sanar da sake bude makarantu daga ranar Litinin, 8 ga Maris, 2021, a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun Sakataren Gwamnatin Jihar, Farfesa Mamma Jibril, a ranar Alhamis, ta ce ya kamata a ba wa dalibai mata Musulmai damar sanya hijabi a duk makarantun gwamnatin jihar.

Sai dai a martani, CAN ta bayyana cewa bata amince da wannan hukuncin da gwamnatin jihar ta yanke ba.

Ta kuma zargi gwamnatin jihar da yanke hukunci a kan wani lamarin da har yanzu yana a gaban kotu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *