fbpx
Sunday, March 7
Shadow

Kungiyar kwallon kafa ta kori ‘yan wasanta 17 saboda sunki amincewa da ragin Albashi

Kungiyar yan wasan kwallon kafa ta Msk Zilina ta kasance daya da cikin kunyoyi masu nasara a Slovakia, kuma kungiyar ta kori yan wasan ta har guda 17 saboda sun ki karbar ragin albashin da aka yi masu ayayin da cutar coronavirus tasa an dakatar da wasanni kwallon kafa.

 

An samu labari daga Board a ranar talata cewa a shafin kungiyar na yanar gizo sun ce rashin amincewar da yan wasan suka yi na ragin albashin ayayin da duniya take cikin rikicin cutar coronavirus ya shafi gasar da suke bugawa kuma yasa an kulle masu filin wasa su. Kuma sun ce rashin biyayya ga kungiyar yasa hakan ya faru. Sun Kara da cewa zasu duba su biya sauran yan wasan abun da ya samu.
Kungiyar ta sanar cewa in aka dawo kan aiki zasu nemi wasu yan wasa daga kungiyar matasa don su cigaba da buga masu wasannin su. Kuma kungiyar ta ce basu zama na farko ba kona karshe a gasar ta Slovakia lig, kuma hakan zai faru ne saboda rikicin cutar Covid-19.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *