Wasan Liverpool da Brighton a yammacin yau ya tashi da sakamakon 1-1. Saidai yana cike da cece-kuce.
A minti 20 da fara wasa, Brighton ta samu bugun daga kai sai gola inda Maupay ya buga mata amma ya barar.
Mohamed Salah da yaci kwallo amma VAR ta kasheta inda Diogo Jota ya ciwa Liverpool kwallo 1. Mane ya ci kwallo amma shima VAR ta kasheta. Ana daf da za’a tashi wasan, Brighton ta samu bugun daga kai sai gola wanda Pascal Gross ya ci mata.