fbpx
Sunday, March 7
Shadow

Luwadi abun kyama ne a musulunci kuma bai kamata a halatta shi ba – Babban Limamin Ghana

Babban Limamin Ghana, Sheikh Osman Sharubutu ya shiga cikin takaddama mai zafi game da luwadi a kasar.

A cikin wata takarda mai shafi 9 wanda Dakta Mohammed Marzuq Abubakari Azindo mai taimaka wa Babban Limamin na Kasa, Sheik Sharubutu ya sanya wa hannu ya ce adawa da al’ummar Musulmi keyi a Ghana kan aikata luwadi ba abin tattaunawa ba ne.

Ya kara cewa, koda yake al’ummar musulmai sun dukufa kan manufofin addini a cikin mulkin kasar, amma luwadi mummunar dabi’a ce wacce Musulunci ke kyama.

Matsayin da kungiyar musulinci ta dauka ya ta’allaka ne akan haifuwa da kuma kyautata rayuwar jama’a ta fuskar hakkin dan-adam.

Sun ci gaba da jayayya cewa a matsayinsu na al’umma, sun zaɓi su goyi bayan jin daɗin al’umma kan haƙƙin mutum.

Luwadi bala’i ne kuma musiba ne, yana daya daga cikin manyan laifuka, kuma yana daga cikin abubuwan da ke kara yaduwar cutar kanjamau a cikin al’umma.

A karshe yace, Luwadi abun kyama ne a musulunci kuma bai kamata a halatta shi ba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *