Wasu fusatattun matasa dake Tashar motar unguwar Jambutu a yankin karamar hukumar Yola ta Arewa dake jihar Adamawa sun hallaka wani barawon waya wanda ake kiran su da ‘yan shila a jihar Adamawa.
Barawon wanda yake cikin babur mai kafa uku sun kama shi ne da makami yana kokarin satar waya, inda nan take suka yi rufa-rufa suka kama shi suka kona shi tare da babur din nasa.
‘Yan shila a jihar Adamawa sun yi kaurin suna wajen yawo da muggan makamai suna sarar mutane suna kwace musu wayoyi. Wanda hakan ya fusata jama’ar yankin Jambutu.