Majalisar dattijai ta nemi gwamnan babban bankin Najeriya, CBN, Godwin Emefiele da kuma daraktan SEC, Lamido Yuguda da su gurfana a gabanta dan ba’asin dalilin dakatar da hadahadar kudaden Internet, Cryptocurrency.
Sanata istifanus Gyang da Tokunbo Abiru ne suka kai kudirin gaban majalisar inda kuma majalisar ta amince da gayyatar wadannan shuwagabannin.
Majalisar ta neki Kwamitin dake kulda da tsaron yanar gizo dana kudi dana kimiyya da fasaha su zauna da Gwamnan CBN da Daraktan SEC su samar da Rahoto akan lamarin.