fbpx
Sunday, April 18
Shadow

Majalisar taraya ta ki amincewa da baiwa kowane dan Najeriya damar rike makami

Majalisar Wakilai ta yi watsi da bukatar dakatar da dokar shugaban kasa, Muhammadu Buhari ta hana mutane daukar makami.

 

Dan majalisa, Uzoma Nkem Abonta ne ya kai kudirin Majalisar saidai Shugaban Masu rinjaye na majalisar, Alhassan Ado Doguwa ya nemi a yi watsi dashi kudirin.

 

Bayan da Dan majalisa, Abonta ya ga cewa, wanna kudiri nasa ba zai samu shiga ba dai ya nemi janyeshi zuwa nan gaba.

 

Saidai kakakin majalisar, Femi Gbajabiamila ya nemi ko dai ya gabatar da kudirin ko kuma ya janye shi gaba daya dan zai batawa mutane lokaci.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *