fbpx
Sunday, March 7
Shadow

Matata maketaciya ce, duk sanda na nemi muyi kwaciyar aure sai ta jika gadon>>Magidanci ya gayawa Alkali

Wani Magidanci, Dauda Adigun ya gayawa Alkali cewa matarsa, Mary Oluwaseun kwata-kwata ta daina ganin kimarsa.

 

Yace shekarunsu 21 da aure amma yanzu in banda cin mutunci babu abinda ke tsakaninshi da ita, kamar yanda ya gayawa Mai shari’a, Ademola Odunade dake kotun Ibadan jihar Oyo.

Ya nemi kotu ta raba aurensu kuma ta bashi damar rike yaransu 4 saboda matar bata kula dasu. Yace sai ta fita aiki sai sanda ta ga damar dawowa kuma bashi da ikon yin magana.

 

Yace hakanan idan ya nemi su yi kwanciyar aure sai taita ihu har sai yara sun ji sannan kuma ta jika gadon da zasu kwanta.

 

An kaiwa matar sammaci har sau 3 amma taki zuwa. A karshe dai alkali ya raba auren inda ya bukaci mijin ya baiwa matar Dubu 5 da zata kwashe kayanta.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *