fbpx
Sunday, April 18
Shadow

Meye hujjarka na cewa ina tattaunawa da wasu mutune domin a kashe ka – Gwamna Bauchi ya gayawa Ortom

Gwamnan Jihar Bauchi Bala Mohammed ya kalubalanci takwaransa na jihar Benuwe, Samuel Ortom, don ya tabbatar da ikirarin da ya yi na cewa shi, Bala, yana tattaunawa da wasu mutane don a kashe shi.

Gwamna ortom a wani taron manema labarai a ranar litinin, 22 ga watan fabrairu, ya yi zargin cewa yana samu barazanar kisa daga makiyaya kuma ya kamata Gwamnan jihar Bauchi ya sani shi zai dauki alhaki idan wani abu ya same shi.

Ortom ya fadi haka ne makonni biyu bayan Gwamnan jihar Bauchi ya yi zargin cewa yana daukar nauyin kai hare-hare tare da bayyana fulanin a matsayin yan ta’adda.

A wata sanarwa da babban hadiminsa na musamman kan harkokin yada labarai, Mukhtar Gidado ya fitar, Gwamna mohammed ya bukaci Gwamna Ortom da ya ba da shaida kan zargin da yake masa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *