fbpx
Sunday, April 18
Shadow

Mijina na lalata da mata a cikin coci>>Wata Ta gayawa Alkali

Wata mata, Mrs Jumai Mala ta kai mijinta, Pastor Ayuba kotu a jihar Adamawa inda ta zargeshi da cewa yana lalata da mata a cikin cocinsa.

 

Tace yana da gado a cikin cocin wanda a cikine yake lalata da matan, tace ta jawo hankalinsa amma sai dai ya rika zagi da yi mata barazana.

 

Tace dan haka ta gaji, tana so Alkalin ya raba aurensu. Tace suna da yara 4 amma babu ruwan mijinta da daukar dawainiyarsu, Itace take komai.

 

Saidai fasto Ayuba ya karyata wannan ikirari inda yace matar tasa sharri ta masa inda har ya gabatar da shaidu 3.

 

Kotun ta daga sauraren karar zuwa 10 ga watan Maris.

 

 

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *