Rahotanni daga Jihar Kogi na nuni da cewa, wani mummunan hadarin mota da ya afku yayi sanadin salwantar rayukan mutane da dama a jihar.
Mutane 14, ciki har da yara biyar ne suka rasa rayukansu a mummunan hatsarin wanda ya faru akan hanyar Anyingba -Ajaokuta dake jihar.
Kwamandan rundunar Hukumar Kiyaye Haddura (FRSC) na jihar, Mista Solomon Aghure shine ya tabbatar da hakan ga manema labarai a Lokoja ranar Juma’a inda ya shaida cewa motoci uku, tare da wasu manyan motoci biyu da motar fasinja ne suka yi hatsarin wanda ya faru da yammacin ranar Alhamis.
Ya kara da cewa, a kalla mutane 14 a cikin mutum 23 ne suka rasa ransu wadanda suka hada da yara Mata guda 3 sai yara maza 2 tare da mata 8 da kuma Namiji daya.