fbpx
Sunday, March 7
Shadow

Najeriya ta fi kowacce kasa yawan matalauta a duniya – Gwamna El-Rufai

Gwamnan jihar Kaduna Nasir El Rufa’i a ranar Talata ya gabatar da Dokar Kare Jama’a ta jihar, yana mai takaicin cewa, Najeriya ta fi kowace kasa yawan matalauta a cikin kasashen duniya.

A cewar El Rufa’i, Najeriya na cikin mawuyacin lokaci, muna da mafi yawan matalauta fiye da kowace ƙasa a duniya.

El Rufa’i ya ce, dole ne a yi amfani da rajistar zamantakewa a cikin shirye-shiryen da aka tsara don taimaka wa talakawa, ya kuma dole ne yan Nageriya su yi watsi da batun bayar da guraben ayyuka ko tallafi ga masu hannu da shuni idan ana son a rage wannan matsalar.

El-Rufai ya kara da cewa, a duk lokacin da Gwamnatin ta bayar da tallafin ko guruben ayyuka sai kaga an baiwa masu hannu da shuni guraben a maimakon talakawan, don haka dole ne mu kaurace wa tunani kuma mu yi amfani da rajistar zamantakewar mu don ba da tallafi ga waɗanda ke buƙatar sa da gaske.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *