fbpx
Tuesday, March 9
Shadow

Ni zaki ne wanda ba za a iya kulle shi a keji ba – Fani-Kayode

 

Tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Femi Fani-Kayode ya mayar da martani game da jita-jitar da ake yadawa na sauya shekarsa daga Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) zuwa All Progressives Congress (APC).

Yace naji wasu na cewa ina tsoron a kaini kurkuku shi yasa nake son komawa APC, bara na gaya maku gaskiya bana tsoron a kamani, saboda ko a lokacin mulkin tsohon Shugaban kasa, Marigayi Umaru Musa Yar’adua anyi kokarin kamani saboda na fadi albarkacin bakina.

Ya kuma ce, shi ya dade yana hulda sosai wasu Gwamnonin Jam’iyyar APC har ma da wasu jiga-jigan jam’iyyar.

Fani Kayode yace shi zaki ne wanda ya wuce a dara mai tarko ya kama sa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *