fbpx
Sunday, April 18
Shadow

NUT tayi barazanar rufe makarantu saboda matsalar tsaro a makarantu

Kungiyar Malaman Makarantu ta kasa (NUT) ta yi barazanar rufe makarantu a duk fadin kasar saboda yawaitar sace-sace da  ‘yan bindiga ke yi a wasu sassan jahohin kasar.

Shugaban kungiyar na kasa Dakta Nasir Idris shine ya bayyana hakan A yayin da yake maida martani game da yawaitar hare-hare a makarantu.

Dakta Nasir ya yi gargadin cewa nan ba da dadewa ba kungiyar zata kira taron kwamitin zartarwa na kasa na NUT don daukar matsaya kan matakin da kungiyar zata dauka.

Ya kuma bukaci Gwamnatin Tarayya da ta dauki mataki ba tare da bata lokaci ba wajan samar da tsaro a dukkan makarantun da ke fadin kasar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *