fbpx
Sunday, March 7
Shadow

Rundunar sojin Sama ta tura dakarunta Katsina dan yakar ‘yan Ta’adda

Rundunar sojin Saman Najeriya tace ta tura dakarunta na musamman jihar Katsina dan taimakawa a fatattaki ‘yan bindigar dake ta’adi a jihar dama yakin Arewa Maso Yamma baki daya.

Rundunar sojin saman ta bakin me magana da yawunta, Air Commodore Ibikunle Daramola ta bayyana cewa tura sojojin ya biyo bayan umarnin shugaban kasa, Muhammadu Buhari ne da kuma tallafawa sojojin da suke a Jihar Katsinar tuntuni da kuma rundunar Operation Hadarin Daji yakar ‘yan ta’addar.

 

Shima da yake magana a yayin tura sojojin, Shugaban sojin Saman, Air Marshal Sadique Abubajar ta bakin wakilinsa, AVM Chales Ohwo ya bayhana cewa aika karin sojojin ya zama dole dan taimakawa sojojin da tun tuni suke can yakar ‘yan ta’addar.

 

Ya kara da cewa, kwanaki 2 da suka gabata tuni rundunar sojin ta fara kai hari ta sama inda ta samu nasarar lalata wata mabiyar ‘yan ta’addar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *