fbpx
Sunday, April 18
Shadow

Rundunar Yan Sanda da hukumar NSCDC Sun Tura Ma’aikata Kaduna da Lagos domin tabbatar da tsaro lokacin bukukuwan karshen shekara

Hukumar Tsaro ta civil defense (NSCDC) a jiya ta ce za ta tura sama da ma’aikata 2500 a jihar Kaduna don tabbatar da sa ido da tsaro a lokacin bukukuwan karshen shekara.

Kwamandan NSCDC a Kaduna, Nurradeen Abdullahi, ya bayyana hakan a wani taro da manyan hafsoshin rundunar.
A wani labarin makamancin wannan, rundunar reshen jihar Legas ta ce ta tura karin‘ yan sanda 1000 domin duba ayyukan barayin hanya.
Amma jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda a jihar, SP Muyiwa Adejobi ya shaida cewa “Kwamishinan’ yan sanda ya tura karin jami’an ‘yan sanda 1000 don kara karfin bangaran kula da harkokin motoci  (MTD) a cikin jihar don inganci kulawa da zirga zirga.”

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *