fbpx
Sunday, April 18
Shadow

Rundunar yan sanda ta damke wasu mutane 48 da ale zargi da satar mutane, fashi da kuma satar shanu

Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta kame wasu mutane 48 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban kamar satar mutane, fashi da makami, damfara ta intanet, da kuma satar shanu.

Da yake gabatar da wadanda ake zargin a Abuja, kakakin rundunar ‘yan sanda Mista Frank Mba ya ce wadanda ake zargin, wadanda suka hada maza 47 da mace daya, an kame su ne a sassa daban-daban na kasar kuma a lokuta daban-daban.

Wasu daga cikin wadanda ake zargin sun hada da Aliyu Suleiman, mai shekaru 26 kuma shugaban kungiyar ‘yan fashi da makami da ke da alhakin kai hari da kuma karbar bindiga daga jami’an‘ yan sanda biyu a kewayen Abuja.

Wani gungun kuma da ake zargin Yusuf Abubakar ya jagoranta kwararre ne a harkar satar mutane kuma shi ke da alhakin sace Mohammed Bashir Bappe, dan majalisar dokokin jihar Taraba.

A karshe Mista Mba, yayi kira ga yan Nageriya da su kiyaye sosai domin a koda yaushe yan ta’adda suna sauya dubarun kai farmaki.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *