Gwamnatin Jihar Abia ta ce da taso ta kai Mista Adeyemi kara kotu amma ta kyale shi saboda kariyar da zauren majalisar dokokin kasar ya baiwa yan sanatoci.
Gwamnatin Jihar Abia ta bayyana Sanata mai wakiltar Kogi ta Yamma a Majalisar Tarayya, Smart Adeyemi, a matsayin wawa kuma wanda bai san abunda yake yi ba.
Wannan ya biyo bayan wasu maganganun da ba su dace ba wanda Sanatan ya yi game da Gwamnan Jihar Abia, Okezie Ikpeazu, a benen Majalisar Dattawa a ranar Talata, inda yace mashaya ne ke mulkin Jihar Abia kuma Gwamna Okezie Ikpeazu, mashayi ne.