Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya ce tattaunawa da ‘yan fashi ba alama ce ta gazawa ba.
Gwamna Matawalle ya fadi hakan ne a ranar Litinin, 22 ga watan Fabrairu, yayin karbar wasu yan bindiga uku da suka tuba suka mika makamansu, kuma sun amince da yarjejeniyar zaman lafiya ta gwamnatinsa.
Ya kara da cewa wannan itace babbar hanyar da za’a iya bi domin magance ta’addanci a Nageriya.