Shehin malamin addinin Islama, Sheikh Dr. Ahmad Gumi ya bayyana cewa satar dalibai da a yanzu ‘yan Bindiga suke yi yafi sauki fiye da yanda a baya suke shiga gari su kashe gaba dayan jama’ar garin.
Yace wanda suka sace daliban Jangebe na yanzu wasu ‘yan Bindiga ne dake kokarin nuna rashin jin dadinsu saboda Gwamnati ta ki sakasu cikin wanda take sulhu dasu.
Yace kuma hakam ya nuna cewa wa’azin da yakewa ‘yan Bindigar na aiki, saboda a baya sukan kashe jama’ar gari gaba daya amma yanzu suna daukar mutanene ba tare da sun ji musu rauni ba.